Mai gadi ya yiwa ƴar gidan da ya ke gadi ciki,
Advertisement
Jami’an ƴan sanda a birnin Lagos sun cafke wani mai gida mai suna Samuel Maikasuwa bisa zarginsa da yiwa ƴar gidan da ya ke aikin gadi ciki.
Samuel Maikasuwa mai kimanin shekaru 20 ya faɗa hannun jami’an tsaron ne bayan da jami’an hukumar yaƙi da masu da cin zarafin yara da marasa karfi su ka cafke shi .
Wannan matashin mai gadi dai ɗan asalin ƙaramar hukumar Abaji ne da ke birnin tarayya Abuja, zai gurfana a gaban Shari’a bayan kammala bincike.
Turawa Abokai
Advertisement